Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «PRNewswire» cewa, Sa'o'i kadan kafin sabuwar dokar da shugaban Amurka Donald Trump ya sanyawa hannu ta hana musulman wasu kasashe shida shiga kasar ta fara aiki, wani akalin kotun tarraya ya yi wasti da dokar.
Alkalin kotun taHawaï, Derrick Watson, ya ce soke dokar zai kaucewa Amurka tafka babban kuskure.
Shugaban kasar Donald Trump wanda ke bayyani a wani taro a birnin Nashville dake kudancin kasar, ya kalubalanci matakin kotun wanda ya danganta da kaucewa hanyoyin shari'a wanda ba'a taba yin irinsa baa kasar.
Mista Trump ya kuma lashi takobin kalubalantar hukuncin a duk inda ya dace har zuwa kotun koli, wanda a cewarsa domin kare 'yan kasarsa.
Shidai alkaliWatson, ya dogara ne akan wasu kalaman Trump, akan musulmai wanda ya ce akwai abubuwa da dama dake nuna kyammar musulmai.
Alkalin dai na la'akari ne da kalaman Trump a lokacin yakin neman zabensa, a lokacin da ya yi firici akan hana musulmi sanya kafa a Amurka muddun ya ci zabe.
Da misalin karfe sha biyu na daren Jiya Laraba ne ya kamata sabon kudirin da Donal Trump ya rattabawa hannu a karo na biyu bayan aiwatar da wasu sauye sauye dake hana musulmin wasu kasasheshiga Amurkar ya kamata ya fara aiki.