Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin fitar da kididdiga a kasar Austria ya bayar da bayani kan sabwar kididdiga da ke nuni da cewa, an samu karuwar kai hari akan musulmi a kasar a cikin wannan shekara fiye da kima.
Bayanin yace a cikin shekara ta 2016 an kai kan musulmi ko kaddarorinsu sai 253, wanda yake nuni da karuwar da kashi 65 idan aka kwatanta da shekara ta 2015.
A wannans hekarar kuwa wadda a halin yanzu ko watanni uku na farkon shekarar basu kare ba, an samu karuwar kai hare-hare a kan musulmi wanda yah aura na shekarar da ta gabata.
Kasar Austria dai na daga cikin kasashen turai da suke karbar baki yan gudun hijira, musamman ma dai daga kasashen da suke fama da rikice-rikicen da aka haddasa a wasu kasashen larabawa.
A cikin wannan makon ne dai aka fitar da sabbin dokoki da suka danganci yan gudun hijira, da nufin kayyade yawan ‘yan gudun hijirar da suke shiga kasar, da kuma daukar matakai na hana yaduwar ayyukan ta’addanci kamar dai yadda mahukunta suke fada.