Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar talabijin ta alalam cewa, mujallar Hafington Post ta kasar Amurka ta buga makalar da ke cewa, a kan idon duniya ake yi wa mabiya mazhabar shi’a kisan kiyashi a sassa na duniya tamkar su ba ‘yan adam ba ne.
Wela Shahin ita ce ta rubuta wannan makala, inda ta yi ishara da kasar Bahrain, inda ake cin zarafin yan shi’a wadanda sune fiye da kashi 70 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar, tare da yi musu kisan kiyashi da korarsu daga kasarsu, da saka su a gidan kaso saboda banbancin akida.
Makalar wadda aka rubuta arnar 17 ga wannan wata na Afrilu ta bayyana cewa, akwai munafunci a cikin abin da wasu kasashen turai ke kira kare hakkin bil adama, inda sukan yi amfani da salon siyasa mai harshen damo, daidai da maslaharsu, kasantuwar sarakunan Bahrain yan korensu ne, duk tak ehakkin bil adama da za su a kan al’ummar kasarsu a wajen turawa ba take hakkin dan adam ba ne.
Haka nan kuma ta yi ishara da hare-haren da aka kai kan fararen hula a cikin makon nan akan fararen hula yan shi’a da aka kwaso daga yankunan Faua da kafarya a Syria, inda ‘yan ta’adda da ke samun dauki da goyon baya daga Saudiyya da Turkiya gami da wasu kasashen turai suka kasha mutane kusan dari da talatin, amma babu wanda ya ce uffan daga cikin wadannan kasashe.
Ta ce baya ga Syria haka lamarin yake a Pakistan, Iraki, Yemen, Najeriya, Bahrain Saudiyya da dai sauransu, inda ake kasha ‘yan kasa saboda kawai su mabiya mazhabar shi’a ne, ba domin sun aikata wani laifi na kisan wani ba.