Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoli (AA) cewa, an fara gyaran wasu daga cikin masallatai da kuma cibiyoyin addini da aka rusa a kasar Bosnia Da Herzegovina a lokacin yakin 1992 zuwa 1995.
Nosrat Abdi Begovich shi ne mataimakin shugaban kasar kan harkokin addini, ya bayyana cewa wasu daga cikin kasashen musulmi ne suka fara bayar da nasu agajin domin gina wasu daga cikin masallatai da cibiyoyin addini da aka rusa a kasar.
Ya ce ya zuwa yanzu wasu daga cikin kasashen msuulmi sun taimaka, amma kuma a hakikanin gaskiya taimakon nasu bai wadatar ba, domin kuwa ba zai isa a iya gyara abubuwan da aka rusa ba, sai dai wasu muhimman daga cikinsu kawai.
Yakin da aka yi tsakanin Bosnia da kuma Saerbia daga ranar 5 ga watan Afirilun 1992 zuwa 14 ga Disamban 1995, ya kawo karshe ne sakamakon cimma yarjejeniya daka yi ta zaman lafiya atsakanin bangarorin biyu.
A wannan yaki an rusa masallatai 832 da kuma cibiyoyin kur'ani guda 69, makabartu 37, sai kuma wuraren tarihi na addini guda 405.