Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo bangaren yada labarai na cibiyar yada al’adun muslunci ya sanar da cewa, karamin ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Uganda tare da hadin gwiwa da gidan radiyon Bilal za su dauki nauyin gasar kur’ani a cikin watan Ramadan mai kamawa.
Musa Mugarwa shi ne babban darakta na gidan radiyon Bilal da ke kasar Uganda,a lokacin da yake zantawa da shugaban ofishin kula da harkokin al’adun muslunci a ofishin jakadancin Iran da ke kasar Ali Bakhtiyari, ya bayyana cewa a bana adadin wadanda za su shiga gasar kur’ania watan Ramadan za su haura na shekarar da ta gabata.
Ya ci gaba da cewa, ya zuwa dukkanin wadanda za su shiga gasar sun riga sun yi rijistar sunayensu, kuma tuni an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan gasa.
Shi ma a nasa bangaren shugaban ofishin kula da harkokin al’adun muslunci na kasar Iran da ke Uganda Ali Bakhtiyari, ya bayyana cewa sun yi farin ciki matuka dangane da irin kokarin da gidan radiyon Bilal yake wajen yada shirye-shrye da suka danganci muslunci.
Ya kara da cewa, za su bayar da dukkanin gudunmawa wajen ganin cewa wannan shirin ya yi nasara, kuma hakan zai kara taimakawa matuka wajen yada lamarin kur’ani a tsakanin musulmin kasar.