Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, marubucin wannan kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta a cikin wannan salo ya yi imanin cewa, wannan shi ne karon farko da aka gabatar da rubutun kwafin kur’ani cikakke a cikin irin wannan salo.
Aikin dai ya dauki tsawon shekara guda ra bi ana gudanar da shi, yayin da shi kuma marubucin a halin yanzu yana da shekaru 80 a duniya.
Wadannan su ne wasu daga cikin irin hotunan wannan kwafin kur’ani da aka watsa a kafofin yada labarai.