Masu gudanar da gangamin sun yi ta rera taken yin Allah wadai da wannan mumman aiki na rusa makabartar da aka rufe da dama cikin iyalan manzon Allah da kuma wasu manyan sahabbansa, makabartar da take tun lokacin manzon Allah ana bizne musulmi a cikinta har lokacin zuwan Wahabya a kan mulkin Hijaz, ta fuskanci danyen aiki daga wahabiyawan inda suka rusa wannan makabarta mai tarihi a muslunci a ranar 8 ga watan Shawwal 1345 bayan hijirar manzo daga Makka zuwa Madina, wanda ya yi dadai da 21 ga watan Afirilun 1925, inda suke zargin musulmi da cewa suna yin shirka a wurin ta hanyar ziyartar iyalan gidan manzon Allah da sahabbansa da aka bizne sua wurin.
Masu gudanar da zanga-zangar musulmi ne na kasar Amurka wadanda suka hada da 'yan asalin kasashen larabawa da Pakistan, Indonesia, Malaysia da ma wasu daga cikin 'yan asalin nahiyar Afirka da sauransu, inda suka daga kwalayen da aka yi rubutu a kansu da ke bayyana akidar wahabiyanci a matsayin babban tunshe dukkanin akidun ta'addanci da sunan addini, na Alkaida, Daesh da sauransu, wadanda suke bata sunan addinin muslunci a idon duniya.