Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da babbar cibiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain ta fitar a yau a cikin shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa masarautar Bahrain tan ayin amfani da salon a kama karya domin rufe bakunan al'ummomin kasar a kan ta'asar da take tafkawa.
Bayanin cibiyar ya ce, masaraytar kasar ta yi amfani da hanyoyi daban-daban da suka saba wa doka wajen cin zarafin 'yan kasa masu hakki a kan dukaknin sha'anin da ya danganci kasarsu, da hakan ya hada da kasha su da kuma kame su da azabtar da su a gidajen kaso saboda bayyana ra'ayoyinsu na siyasa.
Cibiyar ta yi kakakusar suka dangane da salon siyasar munafunci da kasashen turai suke nunawa akan batun kare hakkin bil adama, idan suka yi gum da bakunansu dangane da kisan da ake yi wa al'ummar Bahrain saboda dalilai na siyasa da banbancin mazhaba, ba tare da wata kasar turai ta ce uffan ba kan hakan, saboda alaka da kuma maslaha da ke tsakaninsu da masarautar Bahrain.
Tun kwanakin baya ne jami'an tsaron masarautar kama karya ta Bahrain ta kaddamar da haria a kan gidan babban malamin addini na kasar Ayatollah sheikh Isa Kasim tare da kashe mutane da kuma jikkata wasu a kofar gidansa, tare da tilasta masa zama cikin gida ba tare da fitowa a cikin al'umma ba.