Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Turkiya Alan cewa, Binyamin Alabayarak shugban babbar cibiyar da ke kula da harkokin kur’ani a kasar Turkiya ya bayyana cewa adadin wadanda suka hardace kur’ani a kasar a halin yanzu ya kai dubu 128 idana aka yi la’akari da kididdigar shekara ta 1976.
Ya ci gaba da cewa, akwai shiri da aka yin a kara bunkasa harkokin koyar da kur’ani da hakan ya hada da karatu da kuma harda, wanda hakan yasa ake samun gagarumin ci gaba cikin sauri ta wannan fuska.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, wannan adadin da aka ambata na wadanda suke da rijista nea hukuamnce, wadanda sunayensu ya kai dubu 127 da 440 da ke hannun cibiyar kula da ayyukan kur’ani.
Ya ce cikins hekara ta 2015 adadin masu rijista bai wuce dubu shida ba, a cikin 2014 kuma bai wuce dubu biyar ba, amma yanzu saboda sabon tsari da aka yi ya sanya mahardata da dama suna yin rijista kuma ana sanin da zamansu domin zama karkashin cibiyar.