IQNA

Horar Da Malaman Kur'ani A Kasar Ethiopia

23:02 - July 31, 2017
Lambar Labari: 3481755
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri na horar da malaman kur'ani mai tsarki na kasar Ethiopia a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar.

B.Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, an yanke shawar gudanar da wannan shiri ne bayan ganarwa da ta gudana tsakanin Sheikh Muhammad Saharif babban limamin darika da kuma Hassan Haidari shugaban ofishin yada al'adun muslunci na Iran a habasha

Wanann shiri dai yana samu halartar malaman kur'ani guda 50, wadanda dukkaninsu suna da makarantu da suke koyar da dalibai musulmi karatun kur'ani mai tsarki da sauran ilmomin addini.

Hassan haidari ya bayyana cewa, babbar manufar wanann shiri ita ce samar da yanayi na koyar da kur'ani na zamani mafi sauki ga malaman kur'ani na Ethiopia, domin dalibai musulmi su samu saukin koyon karatun kur'ani da kuma sanin ma'anoninsa alokaci guda.

Wannan da shi ne karon farko da ake gudanar da wani shiri makamancin wanan a karkashin ofishin yada al'adun muslunci na Iran a kasar Habasha, wanda kuma ya samu karbuwa daga dukkanin bangarorin da suke da sha'awar shiga cikin shirin.

3624528


captcha