Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Almanar ta bayar da rahoton cewa, a gobe ne za a gudanar da taron cika shekaru 39 da sace Imam Musa Sadr, wanda cibiyar Imam sadiq (AS) za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Taron zai fara ne daga misalign karfe 20:30 na kasar Lebanon a garin Ansar da ke kudancin kasar Lebanon, tare da halartar malamai da masana da kuma sauran jama’a.
Sheikh Hassan Baghdadi mamba na majalisar shawara ta kungiyar Hizbullah, tare da Sheikh Maher Hammud shugaban kungiyar malaman gwagwarmaya ta duniya, za su gabatar da jawabi.
Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce tunawa da wannan babban malami da aka sace shi da nufin kawo karshen ayyukan da yake yin a neman hadin kan muuslmi da kuma kalu balantar yahudawan sahyuniya.