IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani A Bangaren Tajwidi A Masar

23:46 - August 27, 2017
Lambar Labari: 3481836
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wata gasar kur'ani a bangaren tajwidi da kuam sanin hukunce-hukuncen karatun kur'ani a Masar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Sadl balad cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta Masar ta sanar da cewa za a gudanar da wannan gasa nan ba da jimawa ba.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan shiri yana da matukar muhimamnci, idan aka yi la'akari da cewa karatun kur'ani mai tsarki yana tafiya en tare da tajwidi da kuma sanin hukuncin karatu.

Haka nan kuma ya tabo batun wakokin yabo da ake yin a addini wadanda akasari suna zuwa ne a lokacin tarukan addini daidai da abin da ake yin taro a kansa, kamar yadda kuma akwai salon a bege da ake yi bayan kammala karatun kur'ani ga manzon Allah da iyalan gidansa, wanda hakan sanannen lamari ga al'ummar kasar Masar.

Kasar Masar dai ita ce kasar musulmi da tafi shahara a bangaren karatun kur'ani a duniya, da kuma kyautata shi kamar yadda yake a wajen karatu an tartili ko kuma na rerwa wato tangim.

Wannan gasa dai za ta makaranta matasa daga dukkanin jahohin kasar, inda za a gwada yayin karatunsu da kuma yadda suke kiyaye kaidojin karatu hukunce-hukunce na tajwidi.

3634867


captcha