Bayanin ya ce an gudanar da irin wannan jerin gwano a birane daban-daban na kasar, da suka hada da Shala, Abu Saiba, Almusalla, Shakhura, Karbabad da sauransu.
Wannan gangami da jerin gwano dai ya gudana ne da jijjifin safiyar ranar idi, inda wasu daga cikin matasa suka fara kona tayoyi, da nufin nun arashin gamsuwa da halin da ake ciki a kasar na zama karkashin zaluncin 'yan kama karya.
Masarautar mulkin mulukiyya ta Bahrain dai yanzu haka tana tsare da mutane masu tarin yawa da kame saboda dalilai na siyasa da banbancin mazhaba, bayan kisan wasu da kuma raunata wasu daruruwa.