IQNA

Isra'ila Na Mika Myanmar Makamai Domin Kisan Musulmi

17:37 - September 04, 2017
Lambar Labari: 3481865
Bangaren kasa da kasa, haramtyacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da mika wa gwamnatin Myanmar makamai domin ci gaba da kisan msuulmi da take yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar haaretz ta yahudawa cewa, kisan musulmi da gwamnatin Myanmar ke yi ba zai hana Isra'ila ci gaba da mika mata makamai ba.

A cikin rahoton da wata kungiyar kare hakkin bil adama da gabashin asia ta bayar, ta bayyana cewa ta ji ta bakin daruruwan mutane daga cikin dubban musulmi 'yan kabilar Rohingya da suka tsere daga muhallansu suka shiga cikin kasar Bangaladesh a cikin wannan mako.

Daga cikin mutanen akwai wdanda sun rasa 'ya'yansu, wasu kuma sun rasa iyayensu, wasu sun rasa danginsu, sakamakon hare-haren da sojojin gwanatin Myanmar tare da mabiya addinin Buda masu tsatsauran ra'ayi suka kaddamar a kansu a cikin wannan mako.

Wadanda suka sheda lamarin sun ce jami'an sojin gwamnatin Myanmar sun kai farmaki a ranar Juma'a ashirin da biyar ga watan Agustan da ya kare a kauyen Chut Pyn dake cikin yankinRathedaung, inda suka kashe daruruwan mata da kananan yara, ta hanyar jefa su a cikin wuta suna kona su, kamar yadda kuma sukan yi amfani da manyan adduna wajen sare kawunan duk wani musulmi da suka gani a yankin, sun kona dukkanin gidajen musulmi da ke yankin baki daya, tare da dukkanin kaddarorinsu.

3638258


captcha