IQNA

Za a Gudanar Da Wani Shiri Mai Taken Ghadir A Senegal

17:02 - September 06, 2017
Lambar Labari: 3481869
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani shiri mai taken ghadir a kasar Senegal da nufin kara wayar da kai kan matsayin ahlul bait.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, a cikin makon nan za a fara gudanar da wani shiri na kara wayar da kan musulmi dangane da matsayin ahlul bait (AS) a kasar Senegal.

Wannan shiri wanda zai gudana akarkashin kulawar karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal, zai mayar da hankali ne kan bayani dangane da matsayin iyalan gidan manzon Allaha cikin addinin musunci a garin Fatik mai tazarar kilo mita 130 daga birnin Dakar.

Mutane 40 za su halarci shirin, da suka hada da malaman addini da kuma wasu masana, wadanda dukakninsu suna da gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban addainin muslunci.

Taron zai samu halartar Sayyid Hassan Esmati, shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Iran akasar Senegal, kamar yadda kuma wasu daga jami'ai da masana da za su kasance a wurin bude taron.

3639184


captcha