kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton data fitar yau hukumar kula da yan gudn hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargabar kara tabarbarewar ayukan agaji, inda a cikin sa'o'i ashirin da hudu aka samu 'yan gudun hijira dubu talatin da bakwa da suka tsallake iyaka zuwa kasar ta Bangaladash.
Jagoran ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD cewa da UNHCR ya ce galibin mutatnen na fama da yunwa da kishirwa, ga kuma rashin matsugunni.
Ko baya ga wannan matsala, yanayin rashin lafiyar 'yan gudun hijira na da matukar damuwa, kasancewar ana cikin lokacin damuna.
A baya bayan nan dai shugabar gwamnatinMyanmar Aung San Suu Kyi, na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan kin tsawatawa akan cin zarafin da akewa 'yan kabilar ta Rohingha.
A wani labari kuma a gobe ne ake sa ran ministan harkokin wajen turkiya zai kai ziyara zuwa Bangaladash kan batun 'yan gudun hijira na Rohingha.