IQNA

Haaretz: Majalisar Dinkin Duniya Ta Juya Wa Trump Baya

23:44 - December 22, 2017
Lambar Labari: 3482225
Bangaren kasa da kasa, jaridar yahudawn sahyuniya ta Haaretz ta rubuta cewa, hakika Trump ya ji kunya a majalisar dinkin duniya bayan da aka juya masa baya.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, A kada kuri'ar aka yi a babbann zauren MDD a jiya Alhamis kasashen duniya dari da ashirin da takwas ne suka yi watsi da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka kan birnin Qudus tare da amincewa da si a matsayin fadar mulkin Israi’a.

Zaman da babban zauren MDD ya yi a jiya Alhamis ya zo ne bayan da kudurin yin Allah wadai da matakin da shugaban kasar Amurkan ya dauka kan birnin Qudus ya kasa wucewa a kwamitin tsaro na majalisar a makon da ya gabata, saboda hawa kujera naki da Amurka ta yi.

A zaman kada kuria'ar na jiya dai, duk da cewa kudurin da kasashen duniya 128 suka amince da shi ba zai iya aiwatuwa da karfi ba, amma kudurin ya maida kasar Amurka saniyar ware a duniya.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa kasashe 128 suna goyon bayan Palasdinawa kan zaluncin da Amurka da HKI suka yi na maida birnin Qudus a matsayin babbar cibiyar gwamnatin HKI, duk da cewa wasu kudurorin MDD tun shekara ta dubu da dari tara da sattin da bakwai ba su amince da hakan ba. Sun kuma bukaci a cimma yarjejeniya ne tsakanin bangarorin biyu. 

Kasashe 9 kacal suka goyi bayan Amurka a wannan matsayin da ta dauka. Banda haka wasu kasashen 35 ne suki kada kuri'unsu. 

Kafin a kada kuri'ar dai gwamnatin kasar Amurka ta yi barazana ga duk wata kasa da ta ki amincewa da ra'ayin Amurka a kan wannan batun to zata katse tallafin da take bawa wannan kasar. Amma duk tare da wannan barazanan mafi rinjayen kasashen duniya sun yi watsi da baranar.

Kuri'ar ta babban zauren MDD ta kara maida Amurka saniyar ware a duniya. Sannan wannan yana nuna cewa Amurka ba taisa ta aiwatar da barazanar da ta yi na dakatar da tallafin da take bawa wasu kasashe a duniya ba. Musamman kasashen Jordan da kuma Masar wadanda suke karban tallafi daga Amurka tun da dadewa, kuma hana su wannan tallafi zai gurgurta lamuran Amurka da dama a gabas ta tsakiya musamman a kan wannan matakin da shugaban kasar Amurkan ya dauka kan birnin Qudus.

3675064

 

 

 

captcha