IQNA

Jagoran Juyi:

Manufar Makiya Ita Ce Karya Gwiwar Al’umma Tare Da Raunana Su

22:54 - December 27, 2017
Lambar Labari: 3482243
Bangaren siyasa, A yayin gananarwa da jami'an gwamnati gami da manbobin kwamitin wa'azi na kasar Iran a wannan Laraba, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ita ce ta fi ko wace gwamnati barna da zalinci a Duniya

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Da farko, jagoran ya gabatar da murnarsa na zagayowar ranar haifuwar Imami Hasan Askari (a.s) da kuma zagoyowar ranar yunkurin 9 ga watan Day, ranar da al'ummar kasar suka fito domin karya lagon makiya na makircin da suka kitsa bayan zaben  shugaban kasa na shekarar 2009, sannan kuma ya bayyana cewa goyon bayan da hukumomin Amurka suke bayarwa ga kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya musaman kungiyar nan ta Da'esh, da kuma gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila gami wajen kisan gillar da take yiwa al'ummar Palastinu a ko wata rana, cikekken goyon baya da hadin kan da take bawa hukumar zalinci da kama karya ta masarautar saudiya wajen kisan Al'ummar kasar Yemen, misali ne dake bayyana barna da zalincin hukumar kasar Amurka.

Yayin da yake ishara kan babbanci launi na mahukuntar Amurka da kuma tsarin shari'a na kasar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce duk da irin wadannan matsaloli da kura-kure dake cikin tsarin mashara'antar Amurka, amma wai su ne ke sukan tsarin shari'a na wasu kasashe, musaman ma tsarin shara'ar musulinci na jamhuriyar musulinci ta Iran.

Jagoran ya kara da cewa duk da irin tarin kudaden da hukumomin Amurka suke kashewa domin sanya sabanin siyasa, mazhaba, kabilanci, da harshe ba su ci nasara ba, kuma da yardar Allah, al'ummar kasar Iran da Tsarin musulinci zai ci gaba da kunyata kasar Amurka.

Yayin da yake ishara game da ci gaba da bunkasa da kasar Iran din ke yi ta hanyar juriya da gwagwarmya, jagora ya tabbatar da cewa kasar Iran din za ta ci gaba da bin wannan hanya a lokacin shugaban Amurka na yanzu, kokarin fitar da Iran daga fagen ci gaba ko kuma raunana kasar zai ci gaba da kona zukatansu domin hakan ba zai ci nasara ba.

Jagora ya kara da cewa kokarin da hukumomin Amurka suke yi ba dare ba rana na sanya rikitarwa a dabi'ar dogaro da kai na al'ummar kasar Iran,  ranar 9 ga watan Day wato ranar talatin ga watan Disamban dubu biyu da tara, rana ce da al'ummar Iran ta bayar da amsa game da wannan wasa gami da kare juyin juya halin musulinci.

3676858

 

 

 

 

 

 

captcha