IQNA

22:53 - December 28, 2017
Lambar Labari: 3482246
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro mai taken sulhu a tsaanin al’uma a kasar Sudan tare da halartar masana daga sassa na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka fara gudanar da wani zaman taro mai taken sulhu a tsaanin al’uma a kasar Sudan tare da halartar masana daga sassa na duniya, tare da hadin gwiwa da jami’ar muslunci ta Sudan, da kuma kungiyar bunkasa aladu da ilimin muslunci ta ISESCO gami da kuma jami’ar kasa da kasa ta Afirka.

A yay taron ne wanda yake gudana a birnin Sinar birnin al’adun muslunci na shekarar 2017, ana gabatar da jawabai da malamai da kuma masana suke yi, da nufin kara fadakar da musulmi kan muhimmancin sulhu da zaman lafiya.

Kasar Sudan na daga cikin kasashen Afirka da suke daukar nauyin karatun dalibai na addini, inda suke samun horoa  bangarori daban-daban musamman a bangare kur’ani da kuma harshen larabci da adabinsa

Taron yana samun halartar masana da masu bincik daga kasashe daban-daban da suka hada har da Kenya, Najeriya da kuma Masar.

3676926

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: