IQNA

Adadin Musulmin Amurka Zai Rubanya Daga Nan Zuwa 2050

23:55 - January 04, 2018
Lambar Labari: 3482267
Bangaren kasa da kasa, wani bincike yay i nuni da cewa daga nan zuwa shkaru talatin adadin musulmin amurkazai rubanya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sporting cewa, cibiyar bincike ta pure it ace ta fitar da wannan rahoto, bayan gudanar da wani bincike.

Bayanin ya ce daga nan zuwa 2050 adadin musulmi zai kai miliyan 8 a kasar Amurka, wato kimanin kashi 2.1 na dukkanin al’ummar kasar Amurka.

Wani bincike da aka gudanar a cikin shekara ta 2017 ya nuna cewa yawan musulmi a amurka ya kai miliyan 3, kuma daga nan zuwa 2040 adadinsu zai wuce na yahudawa a Amuka.

Binciken dai ya dogara da kiyasin adadin musulmi da kuma karuwar yan gudun hijira musulmi a kasar da kuma yadda suke haihiwa, hakan ya nuna cewa daga zuwa zuwa shekaru talatin adadin musulmi zai rubanya.

3679087

 

 

captcha