IQNA

Wata Musulma Daga Jahar Michigan Na Hankoron Zuwa Majalisar Dokokin Amurka

23:37 - February 09, 2018
Lambar Labari: 3482381
Bangaren kasa da kasa, Rashida Tulaib wata musulma ce ‘yar majalisar dokokin jahar Michigan wadda ta kudiri aniyar zuwa majalisar dokokin Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Tulaib ta bayyana cewa, idan har ta samu nasar lashe zaben kujerar ‘yar maalisar dokokin Amurka daga jaharta, to za ta zama muuslma ta farko daga wannan jaha da za ta majalisar dokoki.

Ta ci gaba da cewa, babbn abin da ya kara karfafa gwiwarta wajen ganin ta shiga siyasa shi ne, domin ta kare hakkokin muuslmi a cikin Amurka da ma duk inda suke a duniya.

Haka nan kuma ta kara da cewa, shigarta majalisar dokokin dokokin Amurka a Washington, zai bata damar bayyana wa duniya irin halin da masu karamin karfi suke ciki a kasar ta Amurka da kuma masarra rinjaye da suke fuskantar wariya da kyama musamman ma musulmi daga cikinsu.

Ta kara da cewa za ta tsaya kartkahin inuwar jam’iyyarta da Democrat, kuma za ta yi amfani da wannan damar domin yin kyakkyawan wakilci ga wadanda suka zabe ta.

Baya ga Tulaib akwai Firuz Sa’ad wadda ita ma ta kudiri aniyar shiga takarar neman kujerar majalisar dokokin kasar Amurka a zabe mai zuwa.

3689813

 

 

captcha