IQNA

Wata Mata A India Ta Hada Kur’ani Ta Hanyar Dinki A kan Kyalle

23:46 - March 30, 2018
Lambar Labari: 3482524
Bangaren kasa da kasa, wata musulma a kasar India ta gudanar da wani gagarumin aiki na hada kur’ani mai tsarki ta hanyar dinki da zare a kyalle.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Sadal Balad cewa, wata musulma mai suna Nasim Akhtar a yankin Gujrat na kasar India ta gudanar da wani gagarumin aiki na hada kur’ani mai tsarki ta hanyar dinka haruffansa da zare a kyallaye.

Wannan mata ta gudanar da wannan aikin ne a cikin tsawon shekaru 32, inda ta bayyana cewa tana fatan ta yi wani aiki na hidima ga addini ta hanyar barin wani abu mai kima da daraja a cikin addinin musulunci da za a rika tunawa da ita ana yi mata addu’a.

An amfani da kyallen yadi da ya kai dauri guda 12, fadin kyallen ya kai inci 45, kowane inchi ya kai CM2.54, kuma tsawonsa kyallen da aka rarraba ya kai inchi 900.

Abin tuni a nan shi ne Romrud Khan wata ‘yar kasar Pakistan daga yanin Karachi, ta yi wani aiki makamancin wannan inda ita ta rubuta rubuta kur’ani ta hanyar dinka haruffansa  akan kyalle, wanda ya dauke ta shekaru bakawai da rabi.

3702378

 

 

 

 

 

captcha