IQNA

Gungun Malaman Lebanon Ya Jinjina Wa Al’ummar Palastinu Kan Jerin Gwanon Ranar Kasa

23:50 - March 30, 2018
Lambar Labari: 3482526
Bangaren kasa da kasa, gungun malaman addinin muslunci na kasar Lebanon ya jinjina wa al’ummar Palastinu dangane da jajircewa kan hakkokinsu da yahudawa suka mamaye.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga tashar talabijin ta almanar cewa, a yau gungun malaman addinin muslunci na kasar Lebanon ya jinjina ya shirya gangamin nuna wa al’ummar Palastinu goyon dangane da jajircewa kan hakkokinsu da yahudawa suka mamaye da karfin tuwo.

Baya kammala gangamin da malaman suka yi, an karan ta bayanin yin jinjina ga dukkanin al’ummar Palastinu a yankunan zirin Gaza da gabar yamma da kogin Jordan, dangane da raya wannan rana, duk da irin barazanar da Isra’ila ta yi kan hakan.

A yayin jerin gwanon dai yahudawan sahyuniya sun yi ta harbi da bindiga, inda adadi mai yawa na palastinawa suka yi shahada wasu daruruwa suka jikkata, amma duk da hakan ana ci gaba da jerin gwanon a dukkanin yankunan Palastinu.

3702444

 

 

 

 

 

 

captcha