Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Said Abu Ali mataimakin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa ya sanar da cewa, sun dage zaman da ta shirya na gudanarwa na gagagwa domin tattauna batun harin Isra'ila a Gaza a ranar Juma'a da ta gabata.
Ya ce wannan zama an shirya gudanar da shi ranar Litnin, amma saboda wasu dalilai da bai bayyana su ba, ya ce an dage zaman zuwa Talata, domin tattauna batun na kisan gillar da Isra'ila ta yi a Gaza, da kuma daukar mataki.
Kungiyar kasashen larabawan wadda a halin yanzu Saudiyya ke jagorantar ta bisa tsarin karba-karba, ba ta da washiri na gudanar da zama domin tattauna abin da ya faru ko yin Allawadai da hakan, har sai da gwamnatin Palastinu ta bukaci hakan.
Kasashen larabawa da dama dai musamman na yankin tekun fasha suna da alaka ta kud da kud da Isra'ila ta bayan fage, amma a halin yanzu alakar ta bayyana a fili, inda suke ta hankoron ganin sun kulla alaka ta zahiri da Isra'ila.