IQNA

23:57 - May 05, 2018
Lambar Labari: 3482635
Bangaren kasa da kasa, a farkon watan Ramadan mai alfarma ne za a fara gudanar da gasar nan ta kur’ani a tashar talabijin ta alkawthar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar alkawthar cewa, tuni an riga an karbi sunayen sunayen dukkanin wadanda za su shiga cikin wannan gasa daga kasashen duniya.

Na gudanar da gasar ne kai tsaye ta hanyar talabijin, inda a kowace rana ake kayyade adadin mutane da za s shiga da kuma kasashensu da umalokacin da kowannensu zai gabatar da tasa gasar.

Akwai bangaren kir’a, sannan kuma akwai bangaren da ya shafi tafsisri da hukunce-hukuncen karatun kur’ani mai tsarki, wanda duk kai tsaye ne ake amsa tambayoyin.

Haka nan kuma akwai kwamitin alkalai wanda aka kafa, wada ya kunshi alkalai daga kasashen Iran, Iraki, Masar da kuma Syria.

A kowane dare mutane 5 ne daga kasashe 5 za su gudanar da gasar, amma a daren karshe da za a fitar da wadanda za su lashe gasar, mutane 25 da suka isa zuwa mataki na karshe za su kara da juna, inda za a fitar da wadanda suka lase gasar baki daya a dukkanin bangarorin da aka gudanar da ita.

3711388

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: