IQNA

23:08 - May 28, 2018
Lambar Labari: 3482702
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar kur’ani mai taken surat Lukman a cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna na kasar Austria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ana shirin gudana da gasar kur’ani ta surat Lukmana cibibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna nan da makonni biyu masu zuwa.

Wannan gasa dai za a gudanar da ita ne a kan surat Lukman, dangane da abubuwan da surar ta kunsa da kuma abubuwan da take koyar da dan adam na kyawan dabiu.

Yanzu haka dai kofa bude take ga dukkanin wadanda suke da niyar shiga gasar, wadda za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Ramadan mai alfarma.

3717931

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، vienna ، Austria ، surat Lukman ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: