IQNA

23:48 - May 31, 2018
Lambar Labari: 3482710
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar kur’ani mai sarki da ak agudanar a birnin Lagos na tarayyar Najeriya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na National cewa, a jiya ne aka kawo karshen gasar kur’ani mai sarki da ak agudanar a birnin Lagos na tarayyar Najeriya tare da bayar da yautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan gasa ta kebanci daliban jami’a musulmi ne a jahar ta Lagos, inda aka gudanar da gasar tare da halartar daruruwan daliban jami’a.

Gasar ta kunshi bangarori na harda da kuma tilawa, kamar yadda kuma ta tabo wasu bangarori na hukunce-hukuncen karatun kur’ani.

Haruna Sani daya ne daga cikin wadanda suka shirya wannan gasa, ya bayyana cewa babbar manufar hakan ita ce jawo hankalin matasa zuwa ga koyarwar kur’ani mai tsarki, musamman a cikin wannan wata mai alfarma.

Tarayyar Najeriya dai ita ce kasa maifi yawan al’umma a nahaiyar Afirka, kamar yadda kuma akasarin mutanen kasar musulmi ne.

3719287

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: