IQNA

Zaman Taro Tsakanin ‘Yan Sunna Da Mabiyar Mazhabar Shi’a A afirka Ta Kudu

22:38 - June 07, 2018
Lambar Labari: 3482735
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu tsakanin mabiya mazhabar shi’ar Ahlul bait da ‘yan sunna a ranar tunawa da rasuwar Imam Khomeini (RA).

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu tsakanin mabiya mazhabar shi’ar Ahlul bait da ‘yan sunna mai taken hadin kan al’ummar musulmi a mahangar marigayi Imam Khomeini Allah ya kara rahama a gare shi.

Ayatollah Muhammad Hussain Mukhtar shi ne ya gabaar da jawabi a wurin zaman taron, inda ya bayyana mahagar Imam da cewa mahanga ce da take nufin ganin an samu hadin kai tsakanin dukkanin al’ummar muuslmi ba tare da la’akari da wasu bambanbe-bambance na fahimta kan wasu lamurra da ke sakanins ba.

Malamin ya ci gaba da cewa, a kowane lokaci babban burin Imam shi ne ganin an samu fahimtar juna tsakanin al’ummar musulmi, kamar yadda a za a ga haka a cikin kalamansa da jawabansa da rubuce-rubucensa,

Marigayi Imam Khomeini (AS) ya assasa taron makon hadin kan al’ummar musumi da ake gudanarwa a cikin watan rabiul tun daga ranar farko ta haihuwar manzon Allah bisa ruwayar ahlul sunnah har ranar 17 bisa ruwayoyi na ahlul bait, domin ya zama makon ya hada kan dukkanin bangarorin musulmi.

3720776

 

 

captcha