IQNA

23:56 - August 13, 2018
Lambar Labari: 3482889
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da nausawar ad sojojin gwamnatin Syria suke yia  yankunan da ke karkashin ikon ‘yan ta’adda sun kwace iko da Suwaida.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta, sojojin kasar Syria sun fatattaki ‘yan ta’adda da suke iko da yankin Suwaida, daya daga cikin muhimman yankuna da suka fita daga ikon gwamnati.

Yan ta’adda da dama sun mika kansu da makaman da ke hannunsu ga sojojin gwamnatin kasar Syria, yayin da kuma wasu da suka kasa tunkarar sojojin suka tsere.

Sojojin Syria tare da taimakon kasashen Iran da Rasha da kuma kungiyar hizbullah, sun samu gagarumar nasara a kan ‘yan ta’adda da suke samun goyon bayan Amurka da wasu kasashen turai gami da saudiyya da kuma wasu sarakunan larabawa.

3738111

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، syria ، suwaida ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: