IQNA

23:54 - August 17, 2018
Lambar Labari: 3482900
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Saudiyya ta bayar da kudi dalar Amurka milyan 100 ga kawancen Amurka da ke yaki a Syria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a jiya gwamnatin Al Saud ta bayar da kudi dalar Amurka milyan 100 ga kawancen Amurka da ke yaki a Syria domin kafa sansanoni a yankunan da aka kori Daesh.

A zaman da aka gudanar a birnin Brussels na kasar Belgium ne ministan harkokin wajen masarautar Al saud Adel Jubair ya sanar da hakan, inda ya ce za su ci gaba da taimaka ma kawancen Amurka da kudade domin aiwatar da manufofinsa a Syria.

3739072

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Syria ، Amurka ، saudiyya ، daesh
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: