IQNA

23:50 - August 29, 2018
Lambar Labari: 3482934
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron ranar Gadir a kasar Albania.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana shirin gudanar da tarukan ranar Ghadir a kasar Albania tare da halartar dubban mabiya addinin muslunci.

Wannan taro dai ana gudanar da shi a  kowace rana ta goma sha takwas ga watan zul hijja ranar da manzon Allah yay i wasiyyarsa ta karshe a bainar dubban musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa, ranar Ghadir rana mai matukar musulminci ga al’ummar musulmi, domin kuwa a wannan ranar ce manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka ya fayyace makomar addini a bayansa.

A wannan rana ce manzon Allah ya ayyana Imam Ali (AS)  a matsayin wasiyinsa kuma khalifansa a bayansa a gaban dubban sahabbai, kamar yadda wannan ruwaya ta tabbata ga dukkanin bangarorin musulmi, ba tae da la’akari da tawilin da aka yi ta yi wa ruwayar ba daga bisani.

 

3742439

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Imam Ali ، Ghadir ، Albania
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: