IQNA

An Yanke Wa 'Yan rahoton Reuters Daurin Shekaru 7 A Gidan Yari A Myanmar

23:51 - September 03, 2018
Lambar Labari: 3482949
Bangaren kasa da kasa, kotun gwamnatin Myanmar ta yanke hukuncin daurin shekaru 7a gidan kaso a kan 'yan jarida biyu masu aiki da Reuters saboda fallasa wani sirri na kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kotun gwamnatin Myanmar ta yanke hukuncin daurin shekaru 7a  gidan kaso a kan 'yan jarida biyu masu aiki da Reuters saboda fallasa wani sirri da ake boyewa  akasar.

'Yan jaridar su ne Wa lun da shekaru 32 da kuma Kiyau Sui ou da shekaru 27, dukkaninsu an zarge sue n da fallasa wani sirri na gwamnatin kasar da yake a boye.

Wadannan 'yan jarida dai suna gudanar da bincike kan kisan kiyashin da aka yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingya  akasar ta Myanmar, inda suka hardahad bayanai masu matukar hadari akn wannan batu, wadanda za su iya zubar da mtuncin gwanatin kasar tare da saka ta cikin matsala.

3743556

 

 

captcha