IQNA

Erdogan Ya Yi Jawabi Kan Kisan Khashoggi

23:47 - October 23, 2018
Lambar Labari: 3483069
Bangaren kasa da kasa, Cikin wani jawabi da ya gabatar gaban magoya bayansa a wannan talata, Shugaba Erdugan ya yi karin haske kan yadda aka hallaka Jamal Khashoggi a karamin offishin jakasancin Saudiya dake birnin Istambul

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A yayin jawabin nasa, Shugaba Erdogan na kasar Turkiya ya tabbatar da kisan gillar da aka yiwa Jamal Khashoggi dan jaridar na kasar Saudiya da ya yi kaurin suna wajen sukan manifofin yarima mai jiran gado na kasar ta Saudiya Muhamad bn Salman a ranar 2 ga watan Oktoba a cikin  karamin offishin jakasancin Saudiya dake birnin Istambul.

Erdogan ya ce ko shakka babu wannan kisa, abu ne da aka shirya sa tun kafin wannan rana, domin a ranan daya ga watan Octoba akwai tawaga ta musaman da ta zo daga birnin Riyad domin aikata wannan aika-aika.sannan ya tabbatar da cewa kafin aikata wannan kisa an fidda sidin na'urorin da kwada yadda aka aiwatar da wannan kisa, domin hakan wannan shi zai tabbatar da cewa abu da aka shirya a baya.

Har ila yau Erdogan ya soki gwamnatin saudiya da kin amincewa da laifin da ta aikata tun da farko, sai bayan da ta fuskanci matsin lamba daga kasashen Duniya, sannan kuma ya bayar da tabbacin ci gaba da gudanar da bincike har sai an gano hakikanin yadda aka kashe Khashogi da kuma inda a bisne gawarsa.

Daga karshe Shugaba Erdogan ya bukaci kawo gyara a dokar nan ta kare jami'in Diplomasiya, sannan ya ce Kotun Turkiya za ta bi hanyoyin doka domin ganin an hukunta masu laifi.

3758234

 

 

captcha