IQNA

23:52 - October 29, 2018
Lambar Labari: 3483079
Bangaren kasa da kasa, a daren yau ne ake gudanar da taron arbaeen na Imam Hussain (AS) a birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, da kimanin 20:00 na daren yau ne ake gudanar da taron arbaeen na Imam Hussain (AS) a masallacin Anbiya da ke birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha, tare da halartar muuslmi daga bangarori daban-daban.

Wannan taro zai samu halartar malaman addini da aka gayyata da suka hada da malaman sunnah da kuma na shi’a, kamar yadda aka gayyaci wasu masana zuwa taron.

Za a gabatar da jawabai kan matsayin Imam Hussain (AS) da kuma sadaukarwarsa wajen kare addinin da Allah ya aiko kakansa da shi.

Wannan taro dai yan adaga cikin irinsa da aka saba gudanarwa a kowace shekara, amma taron na bana yafi daukar hankali saboda shirin da aka yi kansa.

3759721

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bana ، moscow ، Rasha ، arbaeen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: