IQNA

22:52 - November 15, 2018
Lambar Labari: 3483127
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron maulidin manzon Allah (SAW) a garin Qirawan na kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da wani gagarumin taron maulidin manzon Allah (SAW) a garin qirawan na kasar Tunisia, daya daga cikin garurwa masu tarihi a addinin muslunci.

Wannan taron maulidi na dya daga cikin irinsa da ake gudanar a dukkanin biranan kasar ta Tunisia, wanda bisa ga al'ada akan fara tarukan ne daga lokacin da watan an maulidi ya shigo.

Ma'ikatar kula da harkokin addinin muslunci a kasar na bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin an gudanar da tarukan na maulidin manzon (SAW) a birane da kauyuka.

Malaman addinin muslucni sukan gabar da jawabai kan tarihin manzon Allah (SAW) da kuma irin darussan da suke kunshe a cikin rayuwar tasa mai albarka, wanda dukkanin mutane musulmi da ma wadanda ba musulmi ba za su iya yin koyi da su a cikin rayuwa.

 

3764260

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، rayuwa ، tunisia ، maulidi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: