IQNA

19:50 - November 20, 2018
Lambar Labari: 3483138
A yau ana gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a kasashen duniya daban-daban, na musulmi da ma wadanda ban a muslmi ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kamar yadda aka saba a kowace rana ta 12 ga watan Rabiul Awwal, musulmi suna gudanar da tarukan Maulidin manzon Allah, a wannan shekara ma lamarin yana ci gaba da kara bunkasa a tsakanin al'ummar musulmi.

A kasar Turkiya ana gudanar da irin wadannan taruka a birane daban-daban na kasar, tare da halartar manyan malamai da kuma manyan jami'an gwamnatin kasar.

Kamar yadda haka lamarin yake kasashen Masar da kuma Tunisia gami da Aljeriya da sauransu. Kasashen nahiyar Asia da dama ba a bar su a baya wajen gudanar da irin wadannan taruka, kamar yadda haka lamarin yake kasashen Afrika da dama musamman a yammacin nahiyar, Najeriya dai na daga cikin kasashen da ake bayar da muhimmanci matuka ga wadannan taruka na Maulidin manzon wanda hakan ya sanya aka mayar da ranar ta zama ranar hutu a hukumance.

A kasar Morocco ma sarkin kasar Muhammad na shida da kansa ya halarci wurin taron Maulidin a  yau, kamar yadda shi ma shugaba Assad na Siriya a kowace ranar Maulidin manzon Allah yake halartar wuri tare da jami'an gwanatinsa.

3765708

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، maulidi ، Morocco ، musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: