IQNA

Isra'ila Ce Tushen Dukkanin Matsaloli A Gabas Ta Tsakiya

23:39 - November 25, 2018
Lambar Labari: 3483149
Tsohon Firayi ministan kasar Iraki Nuri Maliki ya bayyana cewa, Isra'ila ita ce tushen dukkanin matsalolin da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Nuri Maliki ya bayyana hakan ne a jiya  alokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban babban taron makon hadin kan al'ummar musulmi, wanda yake gudana a birnin Tehran na kasar Iran tare da halartar malamai da masana daga kasashe 100 na duniya.

Maliki ya ce, dukkanin matsalolin da ake haifarwa a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, Isra'ila tana hannu kai a ciki, inda ya bayar da misali da Palastine, Lebanon, Syria, iraki da kuma Yemen.

Ya kara da cewa, wasu daga cikin kasashen yankin da suke kashe makudan kudade domin rusa kasashen 'yan uwansu an musulmi da larabawa, suna yin hakan ne domin neman yardar Amurka da Isra'ila, kuma abin da suke aiwatarwa shiri ne na Isra'ila.

Dangane da irin tsananin adawar da irin wadannan kasashen suke nuna wa kasar Iran kuwa, Nuri Maliki ya bayyana cewa, Iran ita ce babban karfe kafa da ke kawo cikas ga dukanin manufofin Isra'ila da Amurka a yankin gabas ta tsakiya, dukkanin masu adawa da kasar ta Iran suna adawa ta ita ne saboda wannan dalilin.

3766756

 

captcha