IQNA

Musulmi na Fuskantar Wariya A Wasu Yankuna Na Birtaniya

23:17 - December 05, 2018
Lambar Labari: 3483185
Sakamakon wani bincike ya nuna cewa musulmi suna fuskantar wariya a wasu yankuna na Birtaniya musamman kan batun karbar hayar gidaje.

Jaridar The  Guardian ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, wani bincike da aka gudanar kan yadda musulmi suke rayuwa a wasu yankuna na kasar Birtaniya ya nuna cewa, har yanzu musulmi suna fuskantar matsala da ta shafi nuna musu wariya da bangaranci saboda addininsu.

Cibiyar da ta gudanar da binciken ta hada kai ne da wasu daga cikin ma'aikatan babbar bamayyar cibiyoyin da ke kula da lamurran bayar da hayar muhalli a Birtaniya RLA, inda akan nemi hayar gida ko wurin kasuwanci da sunan Muhammad da farko, daga bisani kuma sai anemi hayar da sunan David.

Sakamakon ya ce an nemi haya da sunan Muhammad sau takwas ana hanawa a cikin yankuna biyar, a daidai lokacin da aka nemi hayar wadannan wurare da sunan David, kuma aka bayar ba tare da wata matsala ba.

Shugaban cibiyar kare hakkin bil adama a Burtaniya ta Human City Institute Coin Galiver ya bayyana cewa, wannan babban abin bakin ciki ne idan har zuwa wannan lokacin musulmi suna fuskantar wariya a Birtaniya.

3769624

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha