IQNA

Ana Ci Gaba Da Aikewa Da Sakonnin Ta'aziyyar Rasuwar Ayatollah Shahrudi

23:51 - December 25, 2018
Lambar Labari: 3483250
Ana ci gaba da mika sakon ta'aziyyar rasuwar marigayi Ayatollah Hashemi Sharudi babban malamin addinin uslunci a ksar Iran, wadanda Allah ya yi masa rasuwa a jiya.

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habrta cewa, ana ci gaba da aikewa da sakonnin ta'aziyyar rasuwar babban malamin addini a kasar Iran Ayatollah Hashemi Shahrudi daga ciki da wajen kasar.

Wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatoci na as ashen musulmi sun aike da sakonninsu ga shugaban kasar Iran, da kuma wasu daga cikin manyan jami'ai, da suka hada da ministan harkokin wajen kasar, kamar yadda shi ma shugaban majalisar dokokin Iran yake ci gaba da samun sakonnin ta'aziyya daga takwarorinsa na kasashne duniya daban-daban.

Ayatollah Hashimi Shahrudi ya kasance shi ne tsohon alkalin alkalai na kasar Iran, kuma ya rasu yana a matsayin shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci a kasar ta Iran.

Ya rubuta littafai masu tarin yawa a bangarori daban-daban na ilimi, da suka hada da bangaren Fikihu, Akhlaq, Tafsir, Hadis, Falsafa da sauransu.

Sakonnin ta’aziyyar Mutanen Lebanon

Sheikh Abdul-amir Qabalan shugaban majalisar koli ta mabiya mazhabar shi’a a Lebanon ya bayyana rasuwar Ayatollah Sayyid Shahrudi da cewa babban rashi ne ga dukkanin al’ummar musulmi, domin an rasa wani jigo daga cikin malamai da suka yi hidima ga addinin muslunci.

Sheikh Qabalan ya mika sakon ta’aziyya ga jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, da kuma iyalan marigayin, da kuma al’ummar Iran baki daya.

Sakon Hizb Da’awah Iraki

Hizbu Da’awah daya daga cikin manyan jam’iyyu na siyasa wadanda aka gina su kan mahanga ta addini ta aike da sakon ta’aziyyar rasuwar Ayatollah sharudi.

Bayanin jamiyyar yace an rasa babban malami wanda ya bayar da gudunmawa  a fagage daban-daban na ilimi, tare da yin addu’a Allah jikansa ya gafarta masa.

3775400

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha