IQNA

18:48 - March 12, 2019
Lambar Labari: 3483450
Majalisar dinkin duniya ta kirayi gwamnatin Afghanistan da kuma kungiyar Taliban da su shiga tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran DID ya bayar da rahoton cewa, majalisar dinkin duniya ta yi kira ga dukkanin bangarorin biyu na gwamnatin Afghanistan da kuam Taliban da su shiga tattaunawar sulhu ba tare da bata lokaci ba.

Wannan na zuwa ne bayan rahoton da bababn manzon majalisar dinkin duniya a kasar Afghanistan Tadamichi yamamatu ya gabatarwa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zaman da kwamitin ya gudanar a jiya.

Bayanin na majalisar dinkin duniya ya ce bababr hanyar kawo karshen matsalar da ake fama da a Afghanistan ita ce shiga tattaunawa kai tsaye tsakanin gwamnatin kasar da kungiyar Taliban, yayin da majalisar diniin duniya ta sha alwashin bayar da dukkanin taimakon da ya kamata domin ganin tatatunawar a tsakaninsu ta cimma nasara.

3797279

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: