Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Reaters ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da taron ne a babban filin da ke wurin hutawa na Hegly da ke kusa da masallacin Nur, wanda daya ne daga cikin masallatan da aka kaiwa harin ta'addanci makonni biyu ad suka gabata.
Taron wanda aka gudanar kafin sallar Juma'a, ya samu halartar dubban mutane musulmi da wadanda ba musulmi ba, da suka hada har da 'yan kasashen ketare ad suka zo domin jajntawa wadanada abin ya shafa.
Haka nan kuma firayi ministar kasar ta New Zealand Jacinda Ardern wadda ta halarci wurin, ta bayyana cewa; dukkanin musulmin da suke a kasar suna hakkin su gudanar da dukkanin lamurransu an addini a cikin 'yanci, kuma ba za su yarda da duk wani aiki na nuna kyama ga musulmi ba.
Ta kara da cewa, hakika abin da ya faru makonni biyu da suka gabata abu ne na bakin ciki a tarihn kasar, wanda ya nuna irin yadda 'yan ta'adda suke da kekasassr zuciya wajen kisan bil adama, musamman ma a masallaci wanda wuri ne abin girmamawa, inda tace gwamnatinta za ta kara tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da cewa an baiwa musulmi kariya a kasar.