IQNA

22:15 - April 07, 2019
Lambar Labari: 3483527
Shugaban mabiya addinin kirista ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis ya bayyana cewa, kasashen Amurka da na turai ne suka jawo mutuwar yara a Afghnistan, Syria da Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran DID na kasar Italiya ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawani a jiya a cibiyar ilimi ta San Carlo da ke kasar Italiya, Shugaban mabiya addinin kirista ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis ya ce; kasashen da suke kera makamai suna sayar da su, su ne ummul haba’isin kisan bil adama a duniya.

Ya ce babban dalilin dukkanin yake-yaken da ake gani a duniya a halin yanzu shi ne, manyan masu kudi da suke suke da kamfanonin kera makamai a a Amurka da kasashen turai, ba za su yi cinikin makamansu ba har sai sun kirkiro yake-yake da kisan al’ummomi a duniya, kuma shi ne dalilin yaki a Afghanistan da Syria da Yemen da sauransu.

Dangane da nuna kyama ga bakin haure kuwa a nahiyar turai, paparoma ya ce babu wani dalilin da zai sanya a nuna kyama ga baki ‘yan ci rani, domin kuwa su kasashen turan ne da kansu suka yi sanadiyyar jawo ‘yan gudun hijira, saboda sun wawushe arzikin wadannan kasashe sun bar su cikin fatara da rashin ayyukan yi.

3801502

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: