IQNA

19:52 - May 07, 2019
Lambar Labari: 3483615
Gwamnatin kasar Sin tana daukar matakai na takura musulmi tare da tauye hakkokinsu na addini musamman a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Al-Dirah ya bayar da rahoton cewa, musulmin kasar Sin suna cikin takura matuka sakamakon irin matakan da mahukuintan kasar suke dauka a kansu, musammana  wannan lokaci na azumin watan Ramadan.

Daga cikin matakan da gwamnatin kasar ta China take dauka, hard a hana musulmi yin azumi a wuraren ayyukan gwamnati, kamar yadda kuma ake tilasta su cin abinci a wuraren ayyuka, bisa hujjar cewa azumi yana sanya musulmin yin kasala wajen gudanar da ayyukansu.

Baya ga haka kuma ana kaa duk wanda ya saba wa wannan doka, tare da daure shia  gidan kaso, inda yanzu haka akwai musulmi da dama da ake tsare da sua  gidajen kurkukun kasar China, bisa laifin sun ki karya azumi.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a kasashen duniya sun sha gargadin gwamnatin kasar China  akan cutar da musulmi, inda a cikin watan day a gabata ma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun shirya wani rahoto kan hakan da suka mika wa kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, domin bin kadun hakkokin musulmi da ake tauyewa  a kasar ta China.

3809436

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kamfanin dillancin labaran iqna ، iqna ، China ، sin ، musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: