IQNA

23:53 - May 11, 2019
Lambar Labari: 3483629
A zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar jiya, ya bukaci dukkanin bangarorin rikicin kasar Libya da su dakatar da bude wuta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a dukkanin mambobin kwamtin tsaron majalisar dinkin duniya, sun amince da kiran dakatar da bude wuta a kasar Libya, tare da komawa kan teburin tattaunawa tsakanin dukkanin bangarorin rikicin kasar.

Babban manzon musamman an majalisar dinkin duniya kan rikicin Libya ne ya gabatar da buktar, inda a jiya Juma'a dukkanin mambobin kwamitin tsaro suka gudanar da zama tare da duba batun.

Tun a ranar 4 ga watan Afirilun da ya gabata ne dai Halifa Haftar, da ke samun goyon bayan Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa da Masar gami da wasu kasashen yammacin turai, ya fara kaddamar da hare-hare kan birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya, da nufin kwace iko da birnin.

Wadannan hare-hare dai ya zuwa yanzu sun yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane, tare da tserewar wasu dubbai daga muhallansu, inda suka zama 'yan gudun hijira a cikin kasarsu

3810302

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bukatar ، Saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: