IQNA

23:49 - May 16, 2019
Lambar Labari: 3483645
Babban baje kolin kasa da kasa na kur’ani na ci gaba da gudana inda aka nuna kur'ani daga Tunisia mai shekaru 247.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, ana ci gaba da gudanar da abbabn baje kolin kur’ai na kasa da kasa karo na ashirin da bakwai a birnin Tehran, inda aka nuna kur'ani daga Tunisia mai shekaru 247 da kuma wasu nauyoyin ayyuka da suka shafi kur’ani.

Tun shekaru ashirin da suka gabata ne aka fara gudanar da wanann baje koli, wanda ake yi a cikin watan Ramadan a babban masallacin Imam Khomenei da ke birnin.

Kamfanoni da madaba’antu na cikin gida da kuam na kasashen duniya, musamman daga kasashen musulmi suna baje kayansu a wurin, inda nuna fasahohin daban-daban da suka hada da nau’oin rubutun kur’ani mai tsarki.

A wanann karon baya ga littafai da kuam tafsirai daban-daban na dukkanin bangarorin musulmi da aka kawo a wurin, akwai sabbin na’urori masu kwakwalwa da aka samar da kur’ani, wadanda ake yin amfani da su wajen koyarwa ko kuma karatu cikin sauki.

Kasar Tunisia na daga cikin kasashen da suka fi nuna nau’oin kwafin kur’ani a wanannbaje kwali, masu wadanda aka rubuta daruruwan shekaru da suka gabata.

3811765

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bangarori ، amfani ، musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: