IQNA

23:51 - May 18, 2019
Lambar Labari: 3483651
Bangaren kasa da kasa, musulmia kasar Afrika ta kudu sun suka kan matakin hana saka hijabia wata makaranta.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai iol.co.za ya bayar da rahoton cewa, musulmi a yankin Sydenham da ke cikin gundumar Durban a kasar Afrika ta kudu sun nuna takaici kan matakin da wata makaranta da ke yankin ta dauka, na hana dalibai mata musulmi saka lullubi.

A cikin wani bayani da cibiyoyin musulmi na yankin da ma wasu yankuna na kasar Afrika ta kudu suka fitar kan batun sun, kirayi mahukunta  a bangaren ilimi da su sanya baki a cikin lamarin.

Faisal Sulamin daya daga cikin jagororin musulmi a kasar Afrika ta kudu, ya bayyana mataki da cewa ya yi hannun riga da abin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bukaci da a baiwa kowane dan kasa damar yin addininsa daidai da koyarwar addinin nasa.

Ya ce saka hijabi ga mata umarni ne na addinin musulunci, a kan ya ce suna kira da babbar murka ga mahukunta da su dauki dukkanin matakan da suka dace domin kare ma musulmi hakkokinsu a fadin kasar ta Afrika ta kudu.

3812570

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Afrika ، hijabi ، musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: