IQNA

23:59 - May 27, 2019
Lambar Labari: 3483679
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani, ya bayyana zaman da Amurka da Isra’ila da sauaran kasashen larabawan tekun fasha za su gudanar kan yarjejeniyar karni da cewa yunkuri ne na kawar da batun Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na farko bayan sake zabensa a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar Iran, Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa, zaman da Amurka ta kira a daya daga cikin kasashen yankin tekun fasha, manufarsa ita ce tabbatar da cewa an kawo karshen duk wani batu na kafa kasar Palastine mai cin gishin kanta.

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu Amurka da Isra’ila suna son aiwatar da wannan shi ne ta hanyar yin amfani da kudaden man fetur na kasashen larabawan yankin tekun fasha, kuma abin takaci wadannan kasashe a shirye suke su bayar da kudinsu domin aiwatar da wanann shiri.

Larijani ya ce mu’amalar karni na a matsayin mika Falastine kyauta ga yahudawan Isra’ila tare da amincewar sarakunan kasashen larabawan yankin tekun fasha, duk kuwa da cewa al’ummar Palastine ta riga ta fayyace matsayinta na kin amincewa da hakan.

Daga karshe ya kirayi al’ummar kasar Iran da su fito jerin gwanon ranar quds kwansu da kwarkwatarsu, domin jaddada goyon bayansu ga al’ummar Palastine.

3814836

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: