IQNA

23:59 - May 31, 2019
Lambar Labari: 3483692
A yau Juma’ar karshe ta watan Ramadan ana gudanar jerin gwanon ranar Quds ta duniya a kasashen Iran da kuma Iraki da Syria da kasashen duniya daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yau dubban daruruwan mutane sun cika titunan birnin bagadaza na Iraki domingudanar da jerin gwanon ranar Quds, wadda a wanann karon take da taken “babu yarjejeniyar karni”.

A kasar Syria ma dubban daruruwan mutane ne suke gudanar da irin wadannan taruka a birane daban-daban na kasar, domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Palestine.

Kamar yadda haka lamarin yake kasar Yemen, da sauran kasashen laraba daban-daban, inda al’ummomi suke fitowa a yau domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Falastine, da kuma bijirewa makircin da ake kitsawa domin kwace masallacin quds a hukumance daga hannun musulmi.

Baya ga kasashen larabawa, ana gudanar da irin wadannan taruka a kasashe daban-daban na nahiyar Afrika da kuma kasashen Asia, gami da kasashen nahiyar turai da ma Amurka, inda dukkanin manufar wadannan taruka dai guda daya ce, ita ce goyon bayan al’ummar Falastinu da ke karkashin mamayar yahudawan Isra’ila.

A taron da aka gudanar a daren jiya garin Gaza, Yahya Sinwar shugaban Hamas a Gaza ya bayyana cewa, suna yin Allawadai dad a abin kunyar da wasu daga cikin shugabannin larabawa suke yi , na hada baki da Amurka da Isra’ila domin cutar da al’ummar Palastine da ma rusa kasashen larabawa da musulmi a  gabas ta tsakiya.

3815984

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: