IQNA

Jagoran Ansarullah: Hare-Haren Martani Sako Ne Ga Al Saud

23:41 - August 18, 2019
Lambar Labari: 3483962
Bangaren kasa da kasa, Abdulmalik Ahuthi jagoran Ansarullah Yemen ya bayyana hare-haren daukar fansa da cewa sako ne ga Al saud.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Abdulmalik Ahuthi Jagoran kungiyar Ansarullah da aka fi sani Alhuthi a kasar Yemen ya gargadi mahukuntan kasar Saudiyya dangane da ci gaba da kaddamar da hare-hare a kan al’ummar kasar Yemen.

A cikin wani jawabi da ya gabatar a jiya wanda gidajen talabijin na ciki da wajen kasar ta Yemen suka watsa kai tsaye, Sayyid Abdulmalik Huthi jagoran kungiyar Ansarullah ya gargadi mahukuntan masarautar Saudiyya da cewa, lokacin yin kisan kiyashi kan al’ummar kasar Yemen ba tare da martani ba ya wuce.

Ya ce hare-haren da jiragen yakin dakarun Yemen suka kaddamar a jiya, su ne hare-haren mayar da martani mafi girma kan Saudiyya da dakarun kasar Yemen suka kaddamar, tun daga lokacin da Saudiyya ta fara kai hari kan al’ummar kasar Yemen shekaru hudu da suka gabata.

Alhuthi ya kara da cewa, dakarun yemen sun harba jiragen yaki marassa matuka guda gomaa lokaci zuwa babbar matatar mai ta yankin Al-shaibah mallakin babban kamfanin mai na Aramco na kasar Saudiyya, wadda ke cikin kasar saudiyya a kusa da iyaka da kasar UAE, da ked a tazarar kilo mita 1100 daga kasar Yemen.

Ya ce wannan na amatsayin babban martani na farko kan kisan mata da kanan yara da rusa masallatai da makarantu da asibitoci da gwamnatin Saudiyya take yi a kasar Yemen, kuma hakan zai ci gaba matukar ba ta dakatar da nata hare-haren ba.

Ya ce yana yin nasiha ga mahukuntan Al saud da su rungumi zaman lafiya da sulhu tsakaninsu da dukkanin al’ummomin yankin gabas ta tsakiya, su daina biye ma Amurka da yahudawa suna ingiza su wajen haddasa yake-yake da fitina a cikin kasashen musulmi da na larabawa.

 

3835634

 

 

captcha