IQNA

23:54 - August 30, 2019
Lambar Labari: 3484001
Bnagaren kasa da kasa, Sojojin kasar Pakistan sun bayar da dama ga ‘yan jarida na kasashen ketare da su ziyarci kan iyakokin kasar da kuma India.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoli cewa, a jiya Alhamis dakarun gwamnatin Pakistan sun yi wa ‘yan jarida na kasashen ketare rakiya zuwa kan iyakokin kasar da India, domin ganewa idanunsu halin da ake cikiayankin, da kuma jin tab akin al’ummomin yankin.

‘Yan jaridar sun isa kauyen Chakutahi da ke cikin Kashmir ta Pakistan, inda suka ji ta bakin mazauna kauyen kan halin da suke ciki, inda suke bayyana cewa suna cikin halin rashin tabbas, sakamakon irin matakan da jami’an tsaron India masu gadin iyakokin kasashen biyu suke dauka.

Daya daga cikin mahukuntan yankin ya shedawa ‘yan jaridar cewa, tun daga farkon shekara ta 2019, ya zuwa jami’an tsaron India sun kashe mutane 19 a kauyen, wasu daga cikinsu ma suna aiki neagonakinsu a lokacin da jami’an tsaron na India suka bude musu wuta.

3838589

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Pakistan ، India ، Kashmir
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: